Wasu ‘yan kasuwar man fetur a sassan Najeriya sun fara canza tambarin kamfanin man fetur na kasa NNPCL a gidajen mansu a daidai lokacin da dillalan ke yanke hulda da NNPC saboda yadda ake gasa tsakanin NNPC da matatar man Dangote.
Jaridar Punch ta rawaito cewa daukar wannan mataki na fara kauracewa kamfanin NNPCL yafi tasiri a Jihar Lagos musamman a baya bayan nan da Dangote ya sake karya farashin litar man fetur.
Tuni wasu dillalan da ke da tambarin NNPCL a gidajen mansu a kusa da yankin Wawa a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, da kuma a Ibafo, da wurare da dama sun cire tambarin NNPCL daga gidajen man su da motocin dakon man fetur mallakinsu.
Wata majiya ta shaida cewa abinda yan kasuwa masu zaman kansu ke bukata a yanzu bai wuce samun isassun kayayyakin da za a samu a cikin farashi mai rahusa,ba musamman a yanzu da matatar Dangote ke yawan sauko da farashin litar man fetur fiye da NNPCL.
Har ila yau, an gano cewa da yawa daga cikin ‘yan kasuwa na iya cigaba da yanke hulda da NNPC saboda rage kudin lodin Man Fetur da matatar Dangote ke yawan yi lokaci zuwa lokaci fiye da kamfanin NNPCL.
Rahotanni sun bayyana cewa an sake samun sauyi da gasa a kasuwar man fetur bayan da matatar mai ta Dangote ta sake rage farashin man daga N950 zuwa 890 kan kowacce lita.
Duk Kokarin jin daga bakin mai magana da yawun kamfanin NNPC, Femi Soneye, domin jin bayanin dalilin da ya sa ‘yan kasuwa ke sauya sheka daga tambarin kamfanin, ya ci tura, domin bai amsa sakon da aka aike masa ta wayar salula ba.
