Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure Rt.Hon Kabiru Alassan Rirum ya tabbatar dacewa daukar matasa aikin damara yanzu ya fara dan ganin matasan yankinsa sun samu ayyukanyi ,sannan an samar da tsaro a Najeriya.
Dan majalisar wanda shine Shugaban kwamatin kula da sojojin sama a majalisar wakilai ta kasa, ya tabbatar da hakan ne a wata ziyara da yakai Kwalejin horas da sojojin sama dake Kaduna.
Yaje Kwalejin ne dan halartar bikin yaye daliban da suka kammala karbar horo,wanda babban hafsan sojojin sama na Najeriya Air Mashar Hassan Bala Abubakar ya jagoranta.
A wata sanarwa da daya daga cikin masu taimakawa Rt. Hon. Kabiru Alasan Rirum,akan harkokin yada labarai wato Hon Fatihu Yusuf Bichi ya fitar a Abuja aka rabawa manema labarai,yace daga cikin matasan da dan majalisar ya shigar aikin sojan saman harda mata.
TST Hausa ta rawaito cewa matasan da suka kammala karbar horo na sojan sama da yawansu yakai 44 ,Alasan Rirum dan jami’yar NNPP ya samu damar samawa matasan yankinsa guda 10 gurbin shiga aikin sojan .
A jawabinsa a wajen taron da akayi ranar Asabar data gabata,babban hafsan sojojin sama na Najeriya Air Mashar Hassan Bala Abubakar ya tabbatar da cewa aikin kare martabar Najeriya ya rataya ne kawai ga daidaikun mutane da ke nuna halaye na musamman da kuma dakarun tsaron Najeriya.
Ya nemi sabbin sojojin saman da su nuna juriya a aikinsu da zasuyi a cikin fararen hula fiye da juriyar da suka nuna a lokacin karbar horo.
Ya kuma shawarcesu da su kiyaye kimar aikin soja da mutuncin aikin , da hidima ga kasa da nagarta a duk inda suka samu kansu.

