Shugaban rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya sauke kansa a matsayin shugaban kamfanin samar da sukari wanda ya kawo karshen shugabancinsa a kamfanin na tsawon shekaru 20.
TST Hausa ta rawaito cewa ajiye aikin da Dangote yayi ya fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Yuni, 2025, a cewar wata sanarwa da sakataren kamfanin,Sukari Temitope Hassan, ya sanyawa hannu.
Duk dacewa babu wata sanarwa dake nuna dalilan attajirin na sauke kansa daga mukamin,amma rahotanni nacewa ta yiyu hakan nada nasaba da hidimomi da aikace aikace da sukayi Aliko Dangote yawa .
Dangote, wanda ya nada kansa a matsayin shugaban kamfanin samar da Sukari tun a shekarar 2005,tunda ga lokacin zuwa yanzu jagorancin sa da samar da kamfanin ya haifar da babban cigaba a kasahen Afurika ba iya Najeriya kadai ba.
Sannan kamfanin ya samar da ayyukan yi ga daruruwan matasa a Najeriya da sauran kasahe makota.
Sanarwar ta kara da cewa, a karkashin jagorancinsa, kamfanin ya aiwatar da muhimman ayyukan hadin gwiwa na baya-bayan nan a jihohin Adamawa, da Taraba da Nasarawa domin inganta samar da sukari a cikin gida da kuma rage yawan shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
Zuwa yanzu Dangote ya amince da Mr Arnold Ekpe, a matsayin sabon shugaban kamfanin samar da Sukari.
Ekpe ƙwararren ma’aikacin banki ne kuma tsohon shugaban ƙungiyar Ecobank, yana da ƙwarewar jagoranci a bangarori daban daban.

