Daga Isah Yusuf Ali
Matatar man fetur din Dangote taci alwashin saukakawa yan Najeriya a kokarinta na cigaba da gogayya da sauran manyan matatun man fetur a Duniya.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da rukunin kamfanonin Dangote ya fitar a shafinsa na X
Sanarwar ta ce domin tabbatar da cewa an rage farashin man fetur a Najeriya kuma shirin samun saukin ya kai ga talakawan Najeriya, Dangote ya sanya hannu da gidan mai na MRS don sayar da man fetur kan naira 935 duk lita daya.
Sanarwar tace tuni aka fara amfani da wannan Sabon farashin a Legas, kuma za a fara amfani dashi daga ranar litinin 23 ga watan Disamba 2024 a sassan Najeriya a gidajen man na MRS.
TST Hausa ta ruwaito cewa, a kwanakin baya matatar man Dangote ta rage farashin mai daga N970 zuwa N899.50 saidai abin takaici yawancin yan kasuwa basa rage farashin yadda ake so a gidajen man su ba.
Tun a baya wasu daga cikin yan Najeriya suke kira ga attajirin na Nahiyar Afurika Alhaji Aliko Dangote da ya bude gidajen man sa na kashin kansa wanda hakan zaisa saukin da yake fata yaje wajen na kasa.

