Masanin sauyin yanayi daga jami’ar fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil Farfesa Muhammad Alhaji ya shawarci manoma a Kano da kewaye da kada suyi gaggawar shuka amfanin gona saboda ruwan da aka samu a daren ranar Juma’a zuwa wayewar garin Asabar.
TST Hausa ta rawaito cewa an dauki tsawon sa’a ana ruwan kamar da bakin kwarya wanda wasu ke Jin cewa kamar damuna ce ta fadi.
Saidai a zantawarsa da tashar Rahma Radio a Kano,shehun malamin yace ba damuna ce ta fadi ba ,saidai alama take yi domin zama cikin shiri musamman manona.
Kamar mai juna biyu ce ta fara nakuda,haka damunar take nunawa ,amma Lokacin faduwar ta baiyi ba.
Yace ko a kwanakin baya a taron fahimtar juna da sukayi tsakaninsu da hukumar Kula da hasashen yanayi ta kasa NIMET a Abuja,ta shaida musu cewa ,ana sa ran damunar bana zata kankama ne a farkon makonni biyu na watan Yuni.
Yace irin wannan ruwa da ake samu a duk farkon damuna da karshenta yana da nasaba da sauye sauyen yanayi.
Tsananin zafi da kai komo da gajimare keyi tsakaninsa da Iska mai kadawa a sararin samaniya na da nasaba da samun irin wannan yanayi na samun ruwan sama lokacin damuna baiyi ba.
“Ina shawartar manona da kada suyi gaggawar shuka ,saboda ba lalle ne ruwan ya dore ba ,Kuma hakan ka iya sawa amfanin gonar da aka shuka da wuri ya kumbura ya lalace a kasa ba tare da ya fito ba”-Inji Farfesa Alhaji.
Gero ne kawai yake jure yanayi na karancin ruwan sama acewar Shehun malamin Farfesa Muhammad Alhaji.

