Tsohon hadimin tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje,a bangaren yaɗa labarai Hon.Shehu Isa Direba ya bayyana cewa maimakon gwamnatin Kano ta mayar da hankali wajen shirya auren zawarawa, ya fi dacewa ta samar da ababen more rayuwa kamar ingantaccen ruwan sha da ilimi ga al’umma.
Hadimin, wanda ya yi wannan bayani a wata tattaunawa da manema labarai a Kano, ya ce shirya auren zawarawa ba shi da cikakken tasiri wajen magance matsalolin rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu, musamman matsalar tattalin arziki da rashin aikin yi.
Ya ce, “Idan ba a samar da ruwan sha ba, ba a inganta ilimi ba, sannan a ce gwamnati na kashe makudan kudade wajen auren zawarawa to a nan ne ake haifar da yara marasa tarbiyya saboda rashin tsari da kulawar iyaye.”
Tsohon hadimin Direba ya kara da cewa gwamnati ya kamata ta zuba jari a fannin da zai haifar da ci gaba mai dorewa, musamman ilimi, da lafiya da samar da ayyukan yi, domin hakan ne kawai zai taimaka wajen rage talauci da inganta rayuwar jama’a.
Wannan jawabi na zuwa ne bayan gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.6 domin shirya auren zawarawa karo na biyu a fadin jihar wani shiri da gwamnati ke cewa zai taimaka wa marasa galihu wajen kafa iyali.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ce auren zaurawa din zai tallafawa mara karfi da wadanda mazajensu suka mutu.

