Wani rahoto ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun kashe sama da naira Tirilyan 1.54 kan giya da wasu nau’ikan abin sha a cikin watanni tara na shekarar 2025.
Rahoton ya samo asali ne daga bayanan kuɗaɗen shiga da manyan kamfanonin giya uku suka gabatar wa kasuwar hannun jari, wato Nigerian Breweries Plc, International Breweries Plc da kuma Champion Breweries Plc.
Bayanan sun nuna cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa Satumba 2025, kamfanonin sun samu wannan adadi ne daga tallace-tallacen giya da sauran abubuwan sha, duk da ƙalubalen tattalin arziki da hauhawar farashi da ake fuskanta a ƙasar.
Daga cikin kamfanonin, Nigerian Breweries Plc ce ta fi kowa samun kuɗin shiga, inda ta kai sama da naira tiriliyan 1 abin da ke nuna cewa kasuwar giya har yanzu na ci gaba da jan hankalin masu saye a Najeriya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/who-ta-yi-kira-da-a-kara-haraji-kan-barasa-da-abubuwan-sha-masu-dauke-da-sikari/
Masana tattalin arziki na ganin wannan rahoto a matsayin alamar yadda mutane ke ci gaba da kashe kuɗi kan abin sha, duk da matsin rayuwa, yayin da wasu ke kallon lamarin a matsayin kira ga wayar da kan jama’a kan tasirin shan giya ga lafiya da tattalin arzikin iyali.
Rahoton ya kuma nuna cewa kasuwar giya a Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙarfi, tare da rawar da take takawa wajen samar da ayyukan yi da haraji ga gwamnati.

