Daga Muslim Muhammad Yusuf(Kaduna)
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakkiya Sanata Lawal Adamu Usman (Mr La) ya gina ajujuwa 100 a fadin kananan hukumomi bakwai na jihar Kaduna.
Kananan hukumomin da suke karkashin dan majalisar kuma suka amfana da aikin gina ajujuwan sun hada da Birnin Gwari,da Chikun,da Giwa,da Igabi,da Kaduna ta Arewa , da Kaduna ta Kudu da Kuma karamar hukumar Kajuru
Yace gina makarantantun furamare da sakandire a mazabarsa yana daga cikin aniyarsa na bunkasa ilimi a yankinsa dama jihar baki daya.
Dan majalisar na jam,iyyar PDP ya kuma ce bunkasa ilimi na daga cikin abinda yasa a gaba kuma yayi alkawari a yayin yakin neman zabensa.
TST Hausa ta rawaito cewa al’ummar yankin sun nuna jin dadinsu da ayyukan raya kasa da wakilin nasu yake gabatarwa.

