Shaharraren malamin addinin Muslunci,na duniya Sheikh Mufti Menk ya baiyana rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin abinda ya sanyashi ya zubar da hawaye.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mufti Menk ya suffanta Buhari da gwarzo kuma jarumi kuma shugaba mai gaskiya.
A cewar Menk, Buhari ba ya wasa da Sallah kuma mutum ne da ya yi wa ƙasa hidima iya iyawar da.
“Rasuwar tasa rashin wani gwarzo, ne a Najeriya”,Inji Mufti
“Mutum ne mai gaskiya, wanda ba ya wasa da sallah, kuma mai tsananin ladabi da biyayya ga addininsa.
Yace ya yi wa mutanensa hidima gwargwadon iyawarsa.
Kuma yace Buhari ya yi shura wajen riko da amana.
“Lalle yana daya daga cikin wadanda suka sa na fara ganin ‘yan Najeriya a wata kyakkyawar fuska,inji Mufti Menk
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ɗaukaka matsayinsa a Aljanna Firdaus. Ameen.
“Allah ya sauƙaƙa wa iyalansa, abokansa da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya,” in ji Menk.

