Gwamnatin tarayya ta ci alwashin karya farashin kayan gine-gine a Najeriya domin saukakawa al’umma.
Ministan kula da gidaje da raya birane na kasa Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana hakan Inda yace an bullo da wani sabon shirin gwamnati na kafa cibiyoyin kera kayan gine-gine a shiyyoyi shida wanda zai rage farashin kayan gini a Najeriya.
Ahmed Musa Dangiwa ya bayyana haka ne a wani taro da Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta shirya tare da masu ruwa da tsaki a fannin gidaje a birnin Legas.
Daily Trust ta rawaito cewa ministan ya ce bunkasa samar da kayan gini a cikin gida zai taimaka wajen rage dogaro da na kasashen waje, wanda hakan zai saukaka farashin gidaje ga ‘yan Najeriya.
Minista Ahmed Dangiwa ya kara da cewa za a kafa wadannan cibiyoyi ne a yankunan da ke da kasuwanni masu girma domin samun saukin kasuwanci da kuma rage matsalar tashin farashin kayan gine-ginen.
Ya ce za a kafa cibiyoyin ne a jihohin Abia, da Ogun da Kwara da Kano da Gombe da Delta, inda kowace cibiya za ta rika samar da kayan gini ga yankinta.
Dangiwa ya ce za’a samar da matakan rage harajin ga masana’antu, da bayar da lamuni mai saukin biya da hakan za taimaka wajen bunkasa fannin gina gidaje a Najeriya.
Haka shima Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Gidaje, Sanata Victor Umeh, ya tabbatar da cewa Majalisa za ta samar da dokoki da manufofi da za su kawo nasarar shirin.
Ya ce Majalisar za ta yi aiki domin ganin an rage haraji, an kuma bayar da tallafi ga masana’antun, da kuma samar da rance mai sauki ga kamfanonin kera kayan gini.

