Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce zaici gaba da baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano goyon baya dan yaki da cin hanci tsakanin jami’an gwamnati da duk wadanda duka ci kudin al’uma.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin kano a lokacin taron ranar yaki da cin hanci da rashawa da aka gudanar.
Majalisar dinkin Duniya ce ta ware duk ranar 12 ga watan Disamba na kowacce shekara dan wayar da man jama’a mahimmacin yaki da cin hanci da rashawa.
TST Hausa ta rawaito cewa kano batayi nata bikin bane saboda a ranar ta 12 ga watan Disamba , Gwamna Yusuf yana bulaguro zuwa kasashen waje.
Gwamna ya nemi hukumar ta yaki da rashawa da karbar korafe korafe taci gaba da aikinta yadda ta sabayi ba tare da tsoro ba.
Ya kuma yabawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano abisa ayyukan da take gabatarwa.
Gwamnan na Kano yace Shugaban hukumar ta anti Corruption Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ciri tuta Kuma kungiyoyin yaki da cin hanci ma na kasa sun yaba masa .
Anasa jawabin tunda farko, Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya nemi hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki dan cimma butakar da ake nema ta yaki da rashawa a Kano
Ya shaidawa gwamna Abba Yusuf cewa hukumar ta gayyato dalibai na Furamare da sakandire dan nuna musu illar cin hanci tun suna yara.
Hukumomin yaki da cin hanci na Najeriya da suka halarci taron sun hada da EFCC,da ICPC da hukumomin tsaro da sauransu .

