Gwamnatin jihar Kano ta nesanta kanta da labarin dake yawo a kafafen sada zumunta da gidajen Radiyon da Talabijin cewa , gwamnatin ta hana kafafen yada shirye shiryen siyasa kai tsaye.
TST Hausa ta rawaito cewa a wani taron fahimtar juna da kwamishinan yada labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya jagaoranta da Shugabannin gidajen Radio da Talabijin na Kano,sun baiwa juna shawarar cewa a takaita yada shirye shiryen siyasa kai tsaye saboda kare mutuncin mutanan Kano abinda ya haifar da ce-ce kuce.
Saidai a wani shirin kai tsaye da gidan Radiyon Guarantee ya karbin bakuncin kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya yace wasu ne suka juya sakamakon tattaunawarsu da Shugabannin gidajen Radio da Talabijin domin cimma wata manufa tasu ko kuma neman tada fitina da neman daukaka.
A cikin shirin, Kwamishinan yace su da kansu Shugabannin kafafen yada labaran suka gabatar da wannan shawara a junansu,kuma a gaban jagororin hukumar kula da kafafen NBC aka gabatar da kudurin,wanda a karshe batun ya zamo shawara ba umarni ba.
Wannan batun ba sabon abu bane ,ace kafafen yada labarai da kansu su daina daukar shirye shiryen siyasa kai tsaye.
Ko wanne gidan radiyo da Talabijin suna da tsarinsu na daukar shirye shiryen siyasa kai tsaye,kafin ma ace gwamnati ta hana.
Kwamishinan ya nemi masu yada Labarai su rika tantance labarai kafin yadawa.
Yace duk tattaunawar da akayi akan shawara aka tsaya ba tursasawa ba ko umarni.

