Manyan ƴan kasuwa da ke shigo da man fetur cikin Najeriya musamman daga kasahen waje sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da rage farashin man fetur da matatar Dangote ke yi a Najeriya.
Wasu daga cikin masu shigo da man sun ce hakan na iya tilasta su sayar da hajarsu a farashin da babu riba, domin masu sayen mai za su fi saye daga inda ya fi araha wato wanda Dangote yayi ragi.
TST Hausa ta rawaito cewa a yammacin jiya Laraba, Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga N890 zuwa N825 a kowace lita, wanda zai fara aiki daga yau, 27 ga Fabrairu.
Dangote yace ya rage litar man fetur din ne albarkacin watan Ramadan na bana.
Wannan ne karo na biyu da Dangote ya rage farashin man a cikin sabuwar shekara watau 2025 kuma karo na uku cikin wata biyu.
Duk da cewa shigo da man fetur daga waje ya ragu, akwai dillalai da har yanzu ake shigo da shi daga kasashen ketare.
Hukumar kula da hada hadar man fetur ta kasa ta tabbatar da cewa kusan kashi 50 cikin 100 na mai da ake amfani da shi a cikin gida har yanzu ana shigo da shi daga waje.
Amma a baya bayan nan Dangote ya tabbatar dacewa yana da wadataccen man fetur din da zai wadatar da yan kasa.
Sai dai yayin da ‘yan Najeriya ke murna da rage farashin, masu shigo da man fetur sun fara damuwa akan matakin da Dangote ke dauka.
Wasu dillalan man fetur da suka nemi a boye sunayensu sun ce matatar Dangote na rage farashi ne don hana shigo da mai daga kasashen waje, kuma hakan na tilasta wa ƴan kasuwa siyar da kayansu babu riba

