Tsohon babban jami’in hada hadarb kudi, na kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL CFO Alhaji Umar Isa-Ajiya, ya musanta zargin cewa ta karfin tsiya jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC suka kama shi ranar Litinin da ta gabata, bisa zargin zamba.
Acikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, tsohon shugaban sashin kudin na kamfanin na NNPC, ya ce sabanin rahotanni dake kara-kaina,a shafukan sada zumunta cewa an kamashi zuwa EFCC Inda tace shi da kansa ya mika kansa ga hukumar, kuma babu wani lokaci da aka kama shi dangane da zargin karkatar da dala biliyan 7.2 na hada-hadar kasuwanci a matatar mai ta Warri da Fatakwal.
“Babu wanda ya kama ni kan zargin badakalar dala biliyan 7.2 dangane a matatar mai, na mika kaina babu tilastwa domin amsa tambayoyi ga hukumar EFCC, daga nan kuma na koma gida, sabanin yadda labarai ke yawo cewa an kama ni bisa zargin zamba” inji shi.
“Ya ce yayi aiki a kamfanin NNPC kuma ya tafi da mutuncinsa, Inda ya nuna makakinsa abisa yadda mutanen ke yada wannan labarin na karya na kamawa da tsare shi domin hakan acewarsa bata masa suna ne kawai suna haka ne
Mista Ajiya ya ce a shirye yake a kowanne lokaci don kare martabarsa da kuma tsawon shekaru da ya yi a hukumar ta NNPC, inda ya ce, “Ina kasar nan kuma a kowacce rana da kuma duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gabansu zan zo”.

