Babbar kotun Jihar kano tayi barazanar daukar mataki mai tsauri ga namu yi mata karen tsaye da kazafi ko karya domin neman suna.
Kotun tace ba zata lamunci kazafi da bata sunanta da ayyukan taba, inda tace zata dauki tsauraran matakai Kan duk wani dake da nufin yin karan tsaye ga ayyukan shari’a a fadin jihar kano.
Babbar kotun na wannan gargadi ne biyo bayan wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sadarwa dake nuna wani magidanci mai suna Sirajo Isa Yarima na kalubalantar hukuncin da wata babbar kotun kano ta yanke nayin gwanjon gidansa sakamakon gaza biyan bashin da ake binsa, inda yake zargin anyi masa rashin adalci.
Kotun ta kara da cewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bada dama duk wanda wani hukunci bai masa dadi ba, yana da damar daukaka kara domin kalubalantar hukuncin maimakon neman tozarta shari’a a bayyanar jama’a.
Idan za’a Iya tunawa babbar kotun Jihar kano karkashin jagorancin Justice Maryam Ahmad Sabo ta saurari wata kara da aka shigar gabanta kan biyan bashi ,wanda bayan baiwa kowane bangare dama tare da tabbatar da mai laifi, kotun ta yanke hukuncin sayar da gidan wanda ake zargi domin biyan bashin da ake binsa bayanda aka kasa samun wata kadara da za’a siyar abiya bashin.
Maimakon daukar mataki na gaba na daukaka kara, wanda ake karar ya fito kafafen sada zumunta yana kalamai marasa dadi ga kotun wanda hakan yaja hankalin babbar kotun.
A yayinda yake zantawa da Wakilin TST Hausa,mai magana da yawun kotunan kano Baba Jibo Ibrahim yace a yanzu haka an bada umarnin a Kamo Surajo Isah Yarima a duk inda yake sabida kalaman raina kotu da yayi.
Baba Jibo yace ita kotu ba wajen wasa bane ko baragada ko wasan Hausa,koma taci barkatai ba, a dan haka dole ya gane cewa kotu sama take da kowa a Najeriya.
Baba Jibo yace abinda magidancin yayi ya saba da sashe na 140 na kundin penal code.
Yace bangaren shari’a a Kano ba zai bar irin wadannan mutanan suna keta haddin shari’a ba,dole ya fuskanci hukuncin dan zama darasi ga yan baya.

