Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana gobe litinin a matsayin daya ga watan Rabi’ul Awwal 1447 bayan hijira.
Wannan sanarwa ta fito ne daga wata takarda da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sultanate, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce, wannan hukunci ya biyo bayan rahotannin da kwamitin ya samu tare da hadin gwiwar kwamitin ganin jinjirin wata na kasa, inda aka tabbatar babu rahoton ganin sabon jinjiri daga kowane bangare na kasar a daren Asabar, 23 ga Agusta, 2025, wanda ya yi daidai da 29 ga Safar 1447AH.
Hakan ya sa aka bayyana cewa Lahadi, 24 ga Agusta, 2025, zai zama cikar kwana 30 na watan Safar, wanda hakan ke nuni da cewa Litinin ce farkon watan Rabi’ul Awwal 1447AH.
TST Hausa ta rawaito cewa tuni ita Kuma Saudiyya ta sanar da yau Lahadi a matsayin daya ga watan Rabbiyul Awwal bayan ganin watan a jiya Asabar.

