Allah yayiwa fitaccen dan kasuwar Najeriya dake birnin Kano Alhaji Aminu Dantata rasuwa a daren ranar Juma’a.
Ya rasu ya na da shekaru 94 da haihuwa a duniya.
An haifi Marigayi Alhaji Aminu Dantata a ranar 19 Mayu na shekarar 1931 ya kuma koma ga Allah a ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2025.
Har zuwa yanzu ba’a sanar da lokacin jana’izarsa ba a hukumance .
Wata makusanciyarsa ta shaidawa TST Hausa cewa ,marigayin ya rasu ne a kasar Dubai.
Ya koma ga Allah yana da yaya 7 da jikoki da dama ,daga cikin yayansa akwai Alhaji Tajuddeen Aminu Dantata sai kuma dan Yar uwarsa fitaccen attijirin Afurika Alhaji Aliko Dangote.
Akwai karin bayani na tare

