Daga Muhammad Ali Yadakwari
Dukiyar hamshakin attajirin nan Aliko Dangote ta haɓaka da ninki biyu a shekarar 2025 zuwa dala biliyan 23.9 kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
A yanzu likkafar attajirin ta daga a duniya Inda ya koma na 86 a cikin jerin wadanda sukafi kuɗi a duniya.
Har yanzu kuma Aliko Dangote shine yafi kowa kuɗi a Afurika.
Idan dai za a iya tunawa, mujallar ta Forbes ta bayyana Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziki a duniya a shekarar 2024 da adadin kuɗi dala biliyan 13.4.
Mujjalar ta Forbes ta kiyasta dukiyar Dangote a kan dala biliyan 23.9,kuma hakan ya samo asali ne saboda kafa matatar man fetur mafi girma da yayi a Afurika da kuma zuba jari sosai da yayi a bangaren harkar man fetur da sauran albarkatun mai a duniya.
Dangote mai shekaru 67,a duniya ya sake zama daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya, mukamin da bai rike ba tun shekarar 2018, a cewar Forbes.
Daga baya ne Dangote ya kara samun cigaba zuwa na 86 daga matsayi na 100 a baya.
Dangote ya kawo cigaba a bangaren harkar man fetur a Najeriya a wani bangaren kuma ya kawo cikas a tsarin man fetur ga gwamnatin tarayya ta hanyar gina matatar mai mafi girma a Afurika Kamar Yadda masana tattalin arziki suka shaida
Matatar man fetur din ta Dangote tana samar da gangar dan yan man fetur 650,000 a duk rana.
Bayan shekaru 11, da zuba jarin dalar Amurka biliyan 23, matatar Dangote ta fara aiki a shekarar data gabata ta 2024.

