Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya taya murna ga kwararrun ‘yan jarida huɗu da aka nada kwanan nan a matsayin shugabanni a manyan gidajen rediyo na jihar.
Wadanda aka nada sun haɗa da Anas Idris Hassan a matsayin Manajan Janar na Vision FM Radio Kano,da Garba Ubale Dambatta a matsayin Manajan Janar na Pyramid FM Radio Kano, da Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu a matsayin Manajan Janar na Nasara FM Radio Kano, da kuma Muhammad Musa Muhammad Inya wanda aka nada a matsayin Manajan Darakta na Hikima FM Radio Kano.
A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya fitar yace a madadin gwamnatin jihar, gwamna Yusuf ya bayyana cewa nadin sabbin shugabannin ya biyo bayan cancanta,da ƙwarewa da sadaukarwar da suka nuna wajen aikin jarida a tsawon shekaru.
Gwamnatin ta bayyana cewa sabbin shugabannin suna da kwarewa da jajircewar da ta dace da manufar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta inganta aikin jarida na gaskiya, na alhaki, da kuma na ci gaban al’umma a Jihar Kano.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin kai da kafafen yaɗa labarai domin ƙara tabbatar da kyakkyawar hulɗa da kuma faɗakar da jama’a game da shirye-shiryen gwamnati da manufofinta.
Sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar yaɗa labarai Sani Abba Yola ya fitar ya nuna cewa gwamnatin ta kuma yi fatan cewa kafafen yaɗa labarai za su ci gaba da yin aiki tare da ita wajen tabbatar da bin ƙa’idodin aikin jarida da kare ingancin bayanai, tare da yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan da ba su da tushe.
A ƙarshe, gwamnatin ta bukaci sabbin shugabannin da su tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci da riƙon amana, tana mai jaddada kudirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da tallafawa kafafen yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa wajen inganta mulki da haɗin kai da jama’a.

