Wata kungiya mai zaman kanta da hadin guiwar kungiyoyin fararen hula sun bukaci a binciki tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Dr Mele Kyari.
Kungiyoyin sun bukaci bincikensa ne kan yadda aka kashe dala miliyan dubu daya da rabi a matatar mai ta Fatakwal ba bisa ka’ida ba
Da yake jawabi yayin taron manema labarai a Abuja, jagoran kungiyar, Michael Omoba, ya yaba da matakin Bola Tinubu na sauke Kyari daga mukaminsa.
Ya ce ya zama dole su jawo hankalin shugabanni na cikin gida da na waje kan zargin babbar sata da aka yi a NNPCL karkashin Mele Kyari.
Omoba ya ce abin takaici ne yadda aka zuba makudan kudi a matatar da bata aiki madadin inganta tattalin arzikin kasa.
Ya ce ya kamata a binciki wannan barna da aka yi da dukiyar jama’a domin tabbatar da adalci ga yan kasa.

