Dilallan man fetur masu zaman kansu sun kara kudin litar mai zuwa N900, daga N890 da ake sayarwa a makon da ya gabata.
Hakan na zuwa ne yayin da aka fara samun tangarda kan cinikin danyen mai da Naira tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPCL.
Bincike ya nuna cewa an wayi gari da ganin karin kudin litar ta man fetur a da yawa daga cikin gidajen man fetur a arewacin Najeriya yayinda kuma gidan man fetur na NNPC suma yawanci ke a rufe.
Karin na da nasaba da tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, wanda ya haura daga $70 zuwa $75, lamarin da ke kara tsadar sarrafa mai a matatun Dangote da na ketare.
Tasirin sayar da danyen mai da Naira Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa matatar Dangote, mai karfin tace gangar mai 650,000 a rana, ba ta sayar da mai ga masu motocin dakon mai a karshen mako ba.
A cewar wani rahoto, lamarin ya shafi wasu kamfanonin man fetur kamar MRS da Ardova, wadanda ke kokarin samun isassun kayayyakin man fetur ta jiragen ruwa daga ketare.
A halin yanzu, kungiyar dallalan man fetur ta bayyana cewa farashin shigo da man fetur ya karu da N88 a cikin sati guda.
Rahotanni nacewa kuɗin litar naira 900 da dillalan suka sanya babu kuɗin dako a ciki.
A ranar 26 ga watan Fabareru shekarar 2025 , matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin litar man fetur daga naira 890 zuwa 825 saboda Azumin Ramadan.

