Gwamnatin tarayya ta sanar da kashe sama da naira miliyan dubu 20 wajen kula da jiragen shugaban kasa.
Wannan na zuwa ne yayin da aka tura sabon jirgin shugaban kasa da aka saye a bara zuwa Afirka ta Kudu domin yin gyare-gyare da canza fasalin jikinsa.
Rahotonnni nacewa a shekarar 2024 kadai, an kashe sama da naira miliyan dubu 14 wajen kula da jiragen, wanda ya kai kashi 71 cikin 100 na kasafin kudin da aka ware wa jiragen.
Rahoton ya ce mafi yawan kudin da aka kashe sun kasance a karkashin sashen kudin da ake ware wa harkokin kasashen waje, kamar sayen fetur da gyaran jirage a kasashen waje.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun tabbatar wa manema labarai cewa an tura sabon jirgin Airbus A330 da aka saye a shekarar 2024 Afirka ta Kudu domin fenti da gyare-gyare.
Jirgi mai shekaru kusan 15 da aka saya akan dala miliyan 100 ya zo ne domin maye gurbin Boeing 737 wanda ke fama da matsalolin gyara.
Wani jami’i ya bayyana cewa an kai sabon jirgin ne don a canza masa fasalin jiki ya dace da matsayin shugaban kasa.
Wata majiya ta ce ana kuma yin wasu muhimman sababbin gyare-gyare a ciki da wajen jirgin domin inganta lafiya da aikinsa.
Ana kashe makudan kudi kan jiragen Najeriya Rahoton ya bayyana yadda gwamnati ke ci gaba da zuba makudan kudi a kan jiragen shugaban kasa tun daga shekarar 2017 zuwa yau.
A shekarar 2017, an ware sama da naira miliyan dubu amma zuwa 2024 an kashe Naira miliyan dubu 20 da rabi karin akan wanda aka kashe a baya.
Masana a fannin sufurin jiragen sama sun alakanta karin kudin da faduwar darajar Naira, da tsadar gyara da kuma tsufan jiragen.

