Kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya ACF ta ce an kusa kai yankin bango a bangaren tsaro.
Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ta tace a taron kwamitinta na koli karo na 78 da ta yi a Jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar Mamman Osuman shi ne ya fadi hakan inda ya yi gargadin yana mai cewa yanzu ba lokaci ba ne da yankin zai zauna ya kame bakinsa ya yi shiru yana ganin irin yadda al.’amura ke ta tabarbarewa a yankin.
Ya yi kira ga shugabannin Arewa da ‘yan yankin da su tashi tsaye su hada kai ganin yadda harkar tsaro ke kara lalacewa da yadda ake ci da gumin yankin da da kuma yadda matsalar muhalli ke kara zama barazana ga yankin gana daya.
Kungiyar ta ce yanzu ba lokaci ba ne da za ta zauna ta zura ido ko ta kawar da kanta da cewa komai yana tafiya daidai a kasar ba.
Osuman ya nuna takaicinsa kan irin rayukan da ake ci gaba da kashewa a kullum a arewacin Najerriyar.
kungiyar ta ACF tace yankin Arewa ya rasa yara matasa maza da mata da tsofaffi a sanadiyyar matsalar tsaro.
A tattaunawarsa da manema labarai mai bayar da shawara ga kungiyar ta ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, a lokacin taron kungiyar da ta yi ,anyi nazari tare da tsokaci kan manyan matsalolin da suke damun Arewa.

