Daga Isha Musa Zage
Wani rahoto kan kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa a duk shekara ya nuna cewa ayyukan gina hanyoyi a karkara da sanya fitilu masu amfani da hasken rana sun lakume sama da naira miliyan dubu 18 a shekarar 2024.
Rahotan ya mayar da hankali kan kashe kudade a Ma’aikatar noma da ma’aikatar tsaro ta tarayya a shekarar 2024 da ake ban kwana da ita.
Rahotan ya bayyana gagarumin saka hannun jari a gine-ginen tituna da samar da fitilu masu amfani da hasken rana da nufin inganta ababen more rayuwa na yankunan karkara da habaka ayyukan noma da akayi a shekarar ta 2024.
Mafi akasarin kudaden an ware su ne ga ayyukan gina hanyoyin a karkara wanda jihar Kano tafi ko wacce jiha amfana.
Daga nan sai jihar Edo ta biyu , Kwara da Kebbi da Nasarawa da suke biye musu baya.
A wata hira da manema labarai, karamin ministan gona Sanata Aliyu Abdullahi yace kuɗaden da aka kashe yawanci suna cikin kudaden tallafi na Dala miliyan 500 da bankin duniya ya bayar, sai Kuma wasu kudaden dala miliyan 100 da gwamnatin tarayya da hadin guiwar gwamnonin jihohi suka bayar a matsayin nasu tallafin.
Rahoton ya nuna cewa a Kano dai kananan hukumomin Bichi da Kunci wacce ta koma karamar hukumar Ghari sune sukafi amfana da gina tinuna da sanya fitilu masu amfani da hasken rana a cikin kananan hukumomin da kuma cikin karakara.
An fitar da kudi sama da naira miliyan 712 a kananan hukumomin guda biyu.
Sai Kuma gina wani titi mai tsawon kilo mita 4 a unguwar Gama cikin karamar hukumar Nasarawa da aka kashe naira miliyan 905 da doriya a shekarar 2024.
Da wani titin Kuma mai tsawon kilo mita 3 da rabi a cikin nasarawa kan titin Limami road wanda shima aka ware naira miliyan 769 da doriya,da sauran aikace aikace a kananan hukumomin kano.
TST Hausa ta lura cewa al’umar da aikace aikace ya shafa ne kadai zasu tabbatar anyi aikin ko ba’a yi ba.

