An kammala aikin bada horo ga maniyata aikin Hajjin bana a Jihar Kano a ranar Lahadi 11 ga watan mayun 2025.
TST Hausa ta rawaito cewa a kalla maniyata 3,155 zasu sauke farali a kasa mai tsarki daga jihar Kano a shekarar 2025.
An kammala aikin ibadar na gwaji ne a sansanin hukumar Alhazai dake birnin Kano,wanda ya samu halartar daruruwan maniyata daga kananan hukumomin Kano 44 da Malaman addini.
A jawabinsa yayin aikin gwajin aikin Hajjin da ya hada da yadda ake Dawafi da jifan Shaidan da zaman Minna da sauransu, gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi maniyatan da su zama jakadu na gari ga jihar Kano a kasa mai tsarki,sannan su yi tsafta da kokarin kare mutuncinsu.
Gwamnan ya tabbatar da cewa a bana alhazan Kano zasu ga sauyi a wajen zamansu da abincinsu da kuma sauran abubuwan da gwamnati tayi musu wanda sai sunje zasu gani.
Gwamna Yusuf ya kuma shaida cewa tallafin kuɗin da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024 ,tayi kari akansu kuma tuni kuɗaden suka isa kasa mai tsarki.
Yace gwamnati zata bada gudun mowar ne domin saukawa alhazan,yana mai cewa sai bayan kammala aikin hajji za’a bada tallafin kuɗin wanda bai bayyana adadinsu ba.
Ya roki maniyatan da suyi takatsantsan wajen yawan kashe kudade daga zuwansu kasar ta Saudiyya.
Gwamna Yusuf ya kuma ce a bana shine zai jagoranci maniyatan zuwa kasa mai tsarki.
Ya tayasu murna tare da fatan zasu kammala aikin hajjin bana lafiya.
A nasa jawabin Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kano,Alhaji Lamin dan Baffa ya godewa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf abisa tallafin da ya baiwa maniyatan da kuma kula da walwalarsu da yayi.
Ranar talata 13 ga watan mayun shekarar 2025 za’a fara jigilar alzahan na Kano

