An gudanar da Sallar Istisqa wato sallar neman ruwan sama a masallacin Annabi Muhammadu SAW da ke birnin Madina da kuma Masjid Haram a Makkah
TST Hausa ta rawaito cewa Sheikh Abdul Bari Al-Thubaity ne ya jagoranci sallar tare da gabatar da huduba ga dubban masu ibada da suka halarta.
Haka kuma an gudanar da makamanciyar sallar a birnin Makkah wato Ka’aba da sauran masallatai a sassan kasar.
An shirya sallar ne bisa umarnin da Masarautar Saudiyya ta bayar, inda aka bukaci al’ummar Musulmi su fito su nemi rahamar Allah da saukar ruwan sama mai albarka, sakamakon yanayin fari da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/rikicin-gaza-sarkin-saudiyya-ya-amincewa-falasdinawa-1000-su-shiga-kasar-su-sauke-farali-kyauta/
A cikin hudubarsa, Sheikh Thubaity ya jaddada muhimmancin tsoron Allah (taqwa), da yawaita istigfari, da komawa ga ayyukan alheri.
Ya tunatar da cewa Allah Shi ne Mai saukar da ruwan sama kuma Mai azurta bayinsa, yana mai kira ga jama’a da su ƙara dagewa wajen addu’a da neman gafara domin samun sauƙi daga ƙunci.
Hakazalika, an gudanar da irin wannan salla a Masjidul Haram da ke Makkah da sauran yankuna daban-daban na Saudiyya, inda malamai suka jagoranci jama’a wajen neman ruwan sama da albarkar Allah.
Sallar Istisqa na daga cikin sunnonin Manzon Allah (SAW), ana gudanar da ita ne a lokutan fari ko ƙarancin ruwan sama, domin neman taimako da rahamar Ubangiji.

