Tsohon Shugaban hukumar kula da tashohin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), Arc Aminu Dabo, ya mika sakon ta’aziyya da juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a mummunan hatsarin mota da ya auku a kusa da Gada, wani yanki da ke kan iyakar jihohin Jigawa da Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 9 tare da jikkatar wasu.
Hatsarin ya faru ne da yammacin Asabar yayin da mutanen ke kan hanyarsu ta komawa gida daga Katsina, inda suka halarci wani bikin aure.
Arc Aminu Dabo, wanda ke daga cikin manyan jiga-jigai a yankin Dambatta Inda mamatan suka fito Wanda kuma shi ne ya mallaki Kwalejin kiwon lafiya ya bayyana lamarin a matsayin mai matukar tayar da hankali, damuwa da ciwo a zuciya. Ya bukaci jama’a da su sanya wadanda suka rasu cikin addu’a, tare da fatan samun sauki da lafiya ga wadanda suka jikkata.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kwalejin , Abdullahi Usman,yace madadin al’ummomin kwalejojin Aminu Dabo gaba ɗaya, ya kuma mika ta’aziyyar sa cikin dumi da girmamawa ga iyalai da duka wadanda abin ya shafa.
A karshe, Arc Dabo ya roki Allah (SWT) da ya jikansu, ya gafarta musu, ya ba iyalansu hakuri da juriyar wannan babban ibtila’i da suka fuskanta.
A halin da ake ciki, a safiyar Lahadi an gudanar da sallar jana’iza tare da binne mamatan a garin Dambatta, inda daruruwan jama’a da manyan mutane suka halarta.

