Hukumar kula da harkokin bunkasa zuba jari ta Jihar Kano, KANINVEST, ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin STATA mai samar da iskar Gas domin aiwatar da shirin samar da iskar gas na CNG a jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen sanya hannun kan wannan yarjejeniya da aka yi a harabar hukumar ta KANINVEST da ke Kano a ranar Juma’a, darakta Janar na hukumar, Muhammad Nazir Halliru ya ce yarjejeniyar ta kai kudi dala miliyan 15.
Shugaban ya bayyana wannan yarjejeniyar a matsayin wani cigaba da zai samar da yanayi mai kyau ta hanyar rage gurbata muhalli da kare lafiyar jama’a da kuma samar da aikinyi ga matasa.
A cewarsa, shirin, idan aka fara aiwatar da shi, zai hada da samar da iskar gas da ake amfani dashi a motocin zamani na CNG a jihar Kano,wanda zai bada dama wajen bude tashohin samar da Iskar Gas din na CNG a Kano.
Halliru ya kuma shaida cewa wannan wata dama ce ta rage tsadar rayuwa ta hanyar rage amfani da man fetur saboda tsadar da yayi wanda hakan zai kawo cigaba a bangaren tattalin arziki musamman a jiha kamar Kano dake da tarihi na kasuwanci.
“Samar da iskar gas din zai shafi motoci ne kadai,sai Kuma tallafawa masana’antu da manyan kamfanonin da ke amfani da CNG din a Kano”Inji Nazir.
Shugaban ya yi watsi da jita jitar cewa fara amfani da wannan yarjejeniyar hadin gwiwar zai kai watanni shida anan gaba.
“Ina tabbatar muku cewa a yanzu haka mun samu amincewar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a dan haka abinda ya rage a gani a kasa”Inji Shugaban
A nasa bangaren, babban jami’in kamfanin na STATA Salman Dantata, ya bayyana jin dadinsa da sanya hannun akan lokacin da ake bukata wanda yace hakan zai taimaka wajen rage tsadar Sufuri da kuma farfado da masana’antun da suka durkushe a Kano.
“Wannan yunƙurin ya yi dai-dai da abubuwan da duniya ke amfani dashi wajen samar da makamashi mai tsafta, da bunƙasa tattalin arziƙi, da dorewar muhalli,Inji Dantata
Dantata yace nan da shekaru biyu masu zuwa za’a ga sauyin da Kano zata samu a bangaren tattalin arziki.
Ya ce nan da shekara daya kamfanin zai fara da babura masu amfani da hasken rana guda 5000 da kuma motoci 10 domin kasuwanci a jihar.
Kamfanin na STATA zai samar da ofishinsa a, garin Dalladi Nasidi,da Maiduguri Road,da titin IBB da Unguwr Shagari Quaters, da Sharada domin saukawa mutane.
Ya bayyana cewa kamfanin zai yi shirin fadada ofisoshinsa zuwa guda 20 a cikin shekaru 5 masu zuwa inda ya kara da cewa hakan zai samar da ayyukayi sama da 300 kai tsaye.

