Kasashen duniyar na cigaba da shirye shiryen shagalin karbar sabuwar shekarar 2026, Rahotanni na cewa a wasu kasashen basa ganin shekarar a lokaci guda saboda bambancin lokacin agogo.
TST Hausa ta rawaito cewa a cikin jerin kasashen duniya, tsibirin Kiritimati ko Kiribati ita ce ke zama ƙasa ta farko a duniya da ta fara shiga sabuwar shekara.
A Kiribati, sabuwar shekarar ta fara a ranar Alhamis da karfe 12:00 na dare wato 1 ga watan Janairun 2026, wanda a Najeriya ya yi daidai da karfe 11:00 na safiyar ranar 31 ga watan Disamba 2025.
Bayan kasar Kiribati, wasu kasashen irinsu Pacific da Gabas sun biyo bayanta.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/mutane-da-dama-sun-mutu-bayan-tankar-man-fetur-da-ta-fadi-a-cunkuson-ababen-hawa-ta-kama-da-wuta-a-enugu/
Sai kasashen New Zealand,da Tonga, da Samoa da suma suka shiga sabuwar shekarar kafin Najeriya da karde 12:00 na rana a gogon na Najeriya wato ranar 31 Disambar 2025.
A yankunan Asiya,kamar China da Singapore za su shiga sabuwar shekarar ne da karfe 3:00 na yamma agogon Najeriya wato a ranar 31 ga watan Disamba 2025, yayin da Japan ta zata shiga da karfe 4:00 na yamma a gogon na Najeriya 31 ga watan Disamba 2025.
A yankin Turai, kamar babban birnin London,da Birtaniya, da su shiga sabuwar shekara ne bayan Najeriya ta shiga da Awa daya wato karfe 1:00 na dare a Najeriya ranar 1 ga watan Janairu 2026, yayin da a Amurka za a shiga da misalin karfe 6:00 na safiya agogon Najeriya ranar, 1 ga watan Janairun 2026.
Najeriya za ta yi maraba da sabuwar shekara daidai karfe 12:00 na dare, ranar 1 ga watan Janairu 2026.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-%e2%82%a610400-kacal-ya-warewa-kowane-%c9%97an-najeriya-a-fannin-lafiyarsa-cikin-kasafin-ku%c9%97in-2026-nma/
Wannan bambanci na lokuta yana nuna yadda lokutan duniya suka kasance daban-daban.
Daga farkon tsibirin Kiribati har zuwa babban birnin New York, wannan tsarin ya nuna yadda duniya ke zagaye cikin lokaci daban-daban.

