Sa’o’i kadan bayan tura tsohon kwamishina a gwamnatin Nasiru El-rufai na jihar Kaduna Bashir Sa’idu, zuwa gidan gyaran hali,Nasiru El-rufai din ya kai ziyara gidan gyaran halin dan ganawa da tsohon kwamishinan.
Ana zargin tsohon kwamishinan kudin da kananan hukumomi na Gwamnatin El-rufai Bashir Saidu da almubuzuranci da kudaden jihar.
El-Rufa’i wanda ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnatinsa, ya kuma je kotun da aka kai Bashir, kara amma bai samu damar ganawa da alkali ba.
Kin ganinsa da Alkalin yayi ,yaja hankalin al’ummar jihar.
A cewar rahotonnni daga nan El-Rufa’i ya kuma je ofishin rundunar sojoji ta Operation Fushin Kada,nan ma bai samu damar gana da jami’an tsaro ba.
A cewar wata majiyar tsaro, gwamnatin kaduna maici karkashin jagorancin Uba Sani na tuhumar tsohon kwamishinan na El-rufai wato Bashir Sa’idu da zargin karkatar da naira biliyan 3.96 da kuma wasu Karin kudade naira miliyan 244 a lokacin da yake rike da mukamin kwamishina a gwamnatin Nasiru El-rufai.
Tsohon kwamishinan ya rike mukamai da dama ciki harda Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin jihar.
Zarge-zargen sun hada da sayar da dalar Amurka miliyan 45 wadanda kudade ne na jihar Kaduna a kan farashin da bai dace ba na Naira 410 kan kowacce dala, maimakon daidai da farashin kasuwa na naira 498 kowacce dala a wancan lokaci.
Sannan akwai zarge zargen na gaza Sanya kudi naira miliyan 244 cikin Asusun jihar,bayan sayar da wasu gidaje a Kaduna,wanda hakan ya saba da sashe na 300 na kundin pinal code na shekarar 2017 a Kaduna
Yayi aiki da El-rufai ne tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Kafin gurfanar dashi a kotu , tsohon kwamishinan shida wasu yan siyasa sun bayyana a gaban majalisar dokokin jihar,amma sun musanta zarge zargen da akeyi musu

