Rahotanni daga sassa daba daban na Najeriya na cewa ana fargabar shiga matsalar karancin man fetur yayin da haramcin amfani da tankoki masu cin lita 60,000 ya fara aiki a yau, 1 ga Maris.
Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa ta sanar da haramta amfani da tankokin a titunan Najeriya a makon da ya gabata.
Kamar yadda Daily Trust ta rawaito hukumar ta ce hakan zai taimaka wajen rage hadurran gobara da asarar rayuka da ke faruwa sakamakon hatsarin motocin dakon mai.
Bayan haramcin da ya fara aiki yau, rahotanni nacewa ba a tsaya iya nan ba domin kuwa za a dakatar da motocin da ke daukar fiye da lita 45,000 daga lodin man fetur a karshen shekarar 2025.
Sai dai, kungiyar masu tankoki ta Najeriya (NARTO), ta nuna damuwa kan matakin, tana mai cewa masu jarin da suka zuba fiye da Naira miliyan dubu 300 a harkar dakon man fetur na iya fuskantar gagarumar asara.
Sakataren kungiyar ta NARTO, Aloga Ogbogo, ya ce suna jiran su ga yadda aiwatar da dokar zata kasance kafin su fadi matsayarsu.
Wasu direbobi sun nuna damuwarsu kan yadda dokar za ta shafi farashin man fetur da kuma aikinsu wadanda suka ce zai iya kaiwa ga sun rasa ayyukansu.

