Kungiyar masu matatun man fetur ta Najeriya (CORAN) ta ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya sauka kasa da N400 idan aka ci gaba da amfani da danyen mai na cikin gida da ake hakowa.
Kungiyar ta kara da cewa daidaita farashin dala zai iya kara sanya farashin man fetur ya karye warwas a Najeriya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa CORAN ta bayyana haka ne yayin da farashin danyen mai ya fadi zuwa dala 65, wanda kuma yake cigaba da karyewa a kasuwannin duniya kuma hakan ke nuni da yiwuwar saukar farashin man da ake amfani da shi a cikin gida Najeriya.
Ana ganin cewa saukar farashi ya zo ne bayan karin hako man da kungiyar OPEC ta yi tare da kakkausar suka kan matsayar gwamnatin Amurka na cinikin mai daga Venezuela.
Jami’in hulda da jama’a na Kungiyar ta CORAN, Eche Idoko, ya ce idan aka kara karfafa aikin matatun man fetur na cikin gida tare da cigaba da samun faduwar farashin danyen mai da saukowar farashin Dala zuwa 50, babu dalilin da zai sa yan Najeriya ba zasuyi fetur akan naira 350 ko kasa da haka.
Idoko ya nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan kasuwa da dillalai ke kokarin hana nasarar tsarin tace mai a cikin gida domin su ci gaba da shigo da man gurbatacce daga waje.

