Gwamnatin tarayya ta dakatar da rokon da tayiwa yan Najeriya na su fara azumin kwana uku a jere da kuma addu’o’i domin neman daukin Allah game da karancin abinci da ake fama da shi a Najeriya.
TST Hausa ta rawaito cewa tunda farko a wata sanarwa da Darakta mai kula da albarkatun noma a ma’aikatar, Misis Adedayo Modupe O ta fitar.,ta ce ma’aikatar ta tura wata tagardar gayyata ga dukinin masu ruwa da tsaki da sauran ma’aikata domin halartar taron adu’oin.
Saidai kuma a cikin wata takardar da ita wannan daraktar ta sake fitarwa a yammacin Asabar tace an dakatar da umarnin yin azumin na kwana uku da adu’oin har sai abinda hali ya yi.
Ba a bayar da wani dalili a hukumance na janyewar ba.
Saidai rahotanni nacewa umarnin fara azumin da adu’oin ya haifar da ce-ce kuce da suka daga yan Najeriya.
Masu sukar sun yi nuni da cewa, ya kamata ma’aikatar ta ba da fifiko kan tsare-tsaren da ya dace da samar da kayayyakin aikin gona, a saukake da tallafawa manoma da inganta tsarin rarraba kayayyaki idan har da gaske take tana son kawo sauyi a bangaren aikin noma

