Majalisar malamai ta Arewancin Najeriya ta nemi Malaman Addinin musulunci su maida hankali akan wasu abubuwa guda biyar a yayinda zasu gababatar da tafsirin karatun Alqu’rani mai tsarki a watan Ramadan na shekarar 2025.
Shugaban majalisar malamai ta Arewancin Najeriya Sheikh Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan a birnin Kano.
Yace abu ne mai kyau a duk lokacin azumin Ramadan malamai masu wa’azi su rika kallon yanayin da jama’a suka samu kansu a ciki wanda hakan zaisa su mayar da hankali akansa lokacin tafsirin karatun Alqu’rani.
Sheikh Ibrahim Khalil yace a bana majalisar malamai na bukatar a mayar da hankali kan abubuwan biyar a yayin wa’azi da suka hada da:
1.Nunawa yan kasa mahimmacin girmama shugabanni.
2.Sanyawa yan kasa kishin kasarsu.
3.Zaburar da shugabanin sanin nauyin dake kansu.
4.Nunawa yan siyasa illar cin mutuncin juna a kafafen yada labarai da na sadarwa.
5.Sai kuma su kansu malaman su yiwa kansu fada domin gujewa yadda yan siyasa ke amfani dasu wajen cimma bukatunsu.
Daga nan malamin ya nemi al’ummar musulmi da kowa yayi rayuwa daidai karfinsa a watan na azumi.
Yace ba abun burgewa bane ,mutum ya tarawa kansa rigima da bukatu masu nauyi a watan na azumi alhalin kuma karfinsa bai kai ba.
Sannan ya shawarci mahukunta da sauran masu hali da su tallafawa duk wanda ya saba taimakon jama’a, musamman wanda a duk azumi yake tallafawa mutane amma wani dalili yasa a bana ya kasa,kuma aka gano shima taimakon yake nema.

