Rundunar sojin Najeriya a karon farko a tarihi ta naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawunta.
Wannan shine karon farko a tarihi da mace ta fara riƙe wannan muƙami tun kafuwar rundunar sojojin.
Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shine karon farko.
Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce zata karɓi muƙamin daga hannun Manjo Janar Onyema Nwachukwu.
Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22 ga watan Afrilun da muke ciki.
Shekaru sama da 50 kenan da kafa rundunar sojin Najeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami.

