Daukar nauyin wallafawa:Magoya bayan El-rufai a Kaduna karkashin jagorancin Hon. Musa Kamilu Kafancan…
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai,zai kasance bako na musamman a tashar ARISE TV domin tattaunawa akan halin da kasa ke ciki.
An shirya tattaunawar ne da karfe 8 na yamma ranar Litinin 24 ga watan Fabarerun shekarar 2025.
El-Rufai wanda ya wallafa a shafinsa na ‘X’ yace: Zan zamo bako a cikin shirin na ARISE TV kai tsaye wanda aka shirya da karfe 8 na dare domin sanar da yan Najeriya halin da kasa ke ciki da matsayin siyasa ta.
El-Rufa’i yace masu bashi shawara akan kafafen yada labarai sun sanar dashi cewa wannan ne karon farko da za’a tattauna dashi a cikin wata kafar yada labarai tun bayan barinsa ofis a matsayinsa na gwamnan jihar Kaduna a 29 ga watan Mayun 2023.
El-Rufa’i a shafin nasa na X ya nemi yan Najeriya su saurari shirin nasa ga masu sha’awa.
A wani labarin kuma El-rufai yace masu adawa dashi sunji kunya a Najeriya bayan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya rayashi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a makon da ya gabata.

