Jam’iyyar NNPP mai alamar littafi a karon farko ta rasa ɗaya daga cikin yan majalisar wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Kasa.
Jaridar Daily Truth ta rawaito cewan dan majalisar tarayyar mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa,wato Hon. Yusuf Shitu Galambi yace ya koma ACP ne saboda rugingimun Shugabanci da yake damun jam’iyar ta NNPP, Acewarsa.
Wannan shine ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC a kasar nan.
A baya bayan nan ma ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Dan majalisar yace Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu sakamakon rigimar Shugabanci tsakanin bangaren dan takarar Shugaban kasa a jami’yar a zaben 2023 Sanata Dr Rabi’u Musa Kwakwanso da wanda ya samar da jam’iyyar wato Dr.Boniface Aniebonam.
Saidai tuni magoya bayan jam’iyyar NNPP mai littafi a Kano sukayi watsi da matakin da dan majalisar ya dauka Inda suke cewa ba sabon abu bane hakan.
A sakon murya da ya aikewa TST Hausa,Hon.Alhaji Nagoda mai taimakawa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf akan harkokin yada labarai,yace watakila kwadayi da neman suna yakai dan majalisar komawa APC.
Yace abin a jajanta masa ne saboda matakin da ya dauka.

