Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta samu ƙarin goyon baya daga manyan yan kasuwa da hukumomi, inda aka tara gudunmawar biliyoyin Naira domin farfado da yankin Arewa.
TST Hausa ta rawaito cewa ana taron na ACF ne a Kaduna domin kaddamar da gidauniyar ceto yankin Arewa.
Zuwa yanzu an Tarawa gidauniyar kuɗi sama da naira biliyan 9.
A cikin tallafin da aka tattara, shugaban rukunin Kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu, tare da Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote, sun bayar da gudummawar Naira biliyan 5.
Haka zalika, tsohon ministan tsaron Najeriya Lt. Gen. TY Danjuma mai ritaya , ya bada Naira biliyan 1, yayin da shahararren ’dan kasuwa Alhaji Dahiru Mangal ya bayar da Naira biliyan 1.
Shugaban rukunin Kamfanin mai na A.A. Rano ya bayar da gudummawar Naira miliyan 100, sannan Majalisar Dattawan Najeriya ta bada Naira miliyan 100.
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, shi ma ya tallafa da Naira biliyan 1.
A cewar ACF, kudaden za su taimaka wajen aiwatar da manyan ayyukan raya Arewa, musamman a fannonin zamantakewa, da ilimi da zaman lafiya, tare da tabbatar da dorewar shirye-shiryen ci gaba a yankin.

