An daura auren Sanatan Kano ta Kudu a majalisar Dattawa ,Abdurrahaman Kawu Sumaila da amaryarsa Hindatu Adda’u Isah a wani keɓantaccen wurin da aka tanada musamman domin gudanar da bikin cikin sirri da natsuwa, ba tare da taron jama’a mai yawa ba.
Amaryar ta kasance sojan Sama a Najeriya.
Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da dukkan shirin auren ne cikin tsari na musamman, wanda ya haɗa da takaitattun manyan baki da suka shaida daurin aure.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Auwalu Abdullahi A.A. Rano, da Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure.
Bikin ya gudana ne cikin kwanciyar hankali, inda aka tabbatar da dukkan sharudda na auratayya bisa koyarwar addinin Musulunci.
Shaidun da suka halarta sun bayyana farin cikinsu da yadda lamarin ya kasance cikin tsari, tare da yi wa ma’auratan fatan zaman lafiya da albarka.
A halin yanzu, ana ci gaba da taya Sanatan murna daga bangarori daban-daban daga abokansa na siyasa, iyalai, abokan hulɗa da kuma jama’ar da ke bibiyar harkokinsa.

