Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sake kubutar da yan Mata guda biyu da ake zargin wani mutum ya yi yunkurin fitarwa zuwa ƙasar Saliyo domin aikatau ko neman kuɗi ba bisa ka’ida ba.
A wani sakon murya da mataimakin babban kwamandan Hisba na jihar Kano Dr.Mujahidden Aminuddeñ Abubakar ya aikewa manema labarai ciki harda TST Hausa, ya ce jami’ansu sun kama wanda ake zargi ne bayan samun bayanan sirri game da shirin tura yaran Yan matan ƙasashen waje ba tare da izini ba.
TST Hausa ta rawaito cewa daya daga cikin yan matan mai suna Zahara’u Audu ta fito ne daga Zaria a Kaduna Mai shekara 16 sai Kuma Kalizah Salim Mai shekara 18 daga Fagge a Kano.
Sanarwar ta ce yan matan, waɗanda ba su kai shekarun yin irin wannan aiki a ƙasashen waje ba, sun amince cewa an musu alkawarin samun “aiki mai kyau” a ƙasar Saliyo, duk da cewa ba su da takardun tafiya da suka dace.
Hukumar Hisbah ta ce an tura batun ga hukumomin tsaro domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Ta kuma tabbatar da cewa za a mika yaran ga iyayensu bayan kammala matakan tsaro da shari’a.
Hukumar ta yi kira ga iyaye da su sanya ido kan ‘ya’yansu, tare da gujewa amincewa da duk wani tsarin aikin ƙetare da ba shi da tsari ko ingantacciyar doka.

