Babban kontirola na hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastam Bashir Adewale Adeniyi, ya ce gwamnatin kasar nan na shirin dakatar da wasu haraji na kwastam kan kayayyakin da ake shigowa dasu cikin kasar nan domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma samar da walwala tsakanin jama,a.
Saidai hukumar ta Kwastam, tace cire harajin kayyakin zaifi shafar kayan da ake shigowa dasu Najeriya daga kasashen Afurika domin dacewa da yarjejeniyar cinikayya ta Afurika wato African Continental Free Trade Agreement.
A yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Adeniyi ya ce Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya baiwa Kwastam umarni na musamman domin ƙarfafa haɗin kasuwanci a Afirka da amfana da damar kasuwanci mara haraji tsakanin ƙasashen nahiyar.
Kontirolan ya bayyana cewa yajejeniyar cinikayya na nufin samar da kasuwar Afirka guda ɗaya ta kaya da ayyuka, inda ƙasashen Nahiyar za su rage haraji a hankali har su kai kayan da ba,a karbar haraji a cikinsa wato (zero duty), domin kayan da aka samar a Afirka su samu damar shiga kasuwanni ba tare da biyan haraji ba.
Ya kuma ce lokacin aiwatar da yarjejeniyar, akwai abubuwan da za a kula da su kamar dokokin asalin kaya, da rahotannin fifiko na kasuwanci, da dakatar da haraji kan kayayyakin da ake musayar su tsakanin ƙasashen memba.
Adeniyi ya amince cewa wasu ƙoƙarin haɗin gwiwa a baya, ciki har da na ECOWAS, sun fuskanci ƙalubale wajen aiwatarwa, don haka Najeriya ba za ta so a maimaita irin wannan matsala ba. Ya ce hukumar Kwastam za ta kasance cibiyar aiwatar da AfCFTA a ƙasar.

