Babban malamin Addinin musulunci a Kano kuma daya daga cikin Limaman masallacin Juma’a na Al-Ikhlas Farfesa Mansur Isah Yelwa ya nemi jama’a da su rika kaucewa ayyukan Riya wato aiki ba Dan Allah ba ,Yana Mai cewa komai girman aiki ba domin Allah ba ,baya amfanar da Mai aikin.
A yayin hudubarsa ta ranar Juma’a a sabon masallacin na Sharada, Farfesa Mansur Yelwa ya bayyana cewa an sanya wa shi kansa masallacin suna “Al-Ikhlās” ne domin tunatar da al’umma muhimmancin yin aiki don Allah kaɗai ba tare da son zuciya ba.
Farfesa Yelwa ya ce sunan Al-Ikhlās na ɗauke da babbar manufa ta tsarkake niyya, tare da jaddada cewa masallaci ba kawai wurin ibada ba ne, har ila yau hanya ce ta gina zuciya da tarbiyyar al’umma.
Ya bayyana cewa jama’a su sanya a ransu cewa dukkan ayyuka ko a masallaci ko a cikin mu’amala su zama don yardar Allah.
Ya kuma yi kira ga mazauna Sharada da su yi amfani da sabon masallacin wajen ƙarfafa zumunci,da wayar da kai, da karɓar ilimi cikin natsuwa.
A ƙarshe, Farfesa Yelwa ya yi addu’ar Allah ya sanya masallacin Al-Ikhlās ya zama tushen shiriya, da hanyar ƙarfafa haɗin kan musulmi a Arewacin Najeriya da kasa baki daya

