Kungiyar Masana Kimiyyar Ruwa ta Najeriya, wato Nigeria Association of Hydrological Sciences (NAHS), ta kammala taron shekar – shekara na 2025 a jami’ar Bayero da ke Kano, inda aka gudanar da zaben sabbin shugabannin ƙasa na kungiyar.
A yayin zaben da ya gudana cikin lumana da gaskiya, Farfesa Injiniya Luke O. Uzoigwe (FNAHS) ya fito a matsayin sabon Shugaban Ƙasa na kungiyar.
Sauran shugabannin da suka lashe kujeru sun haɗa da:
Mataimakin Shugaba na Ɗaya: Farfesa Shakirudeen Odunuga (FNAHS)
Mataimakin Shugaba na Biyu: Farfesa Maxwell Ocheri (FNAHS)
Mataimakin Shugaba na Uku: Dr. Tasi’u Y. Rilwanu.
Sakatare Janar: Dr. Joel Efiong.
Mataimakin Sakatare Janar: Kabir Aminu.
Ma’ajin Kuɗi: Abubakar Ismail (FNAHS).
Sakatare na Kuɗi: Eremen E. Esta.
Sakatare na Yaɗa Labarai: Yakubu Yusuf.
Rahotanni sun bayyana cewa zaben ya gudana cikin natsuwa da gaskiya, lamarin da ya jawo yabo daga mahalarta taron.
Sabon shugaban kungiyar, Farfesa Uzoigwe, ya yi alkawarin ƙarfafa haɗin kai, ci gaba da bincike da bunƙasa ƙwarewar masana a fannin samar da ruwa a Najeriya da inganta bangaren, albarkatun ruwa da kula da muhalli a Najeriya.
Kungiyar NAHS tana daga cikin muhimman ƙungiyoyin kimiyya a ƙasar da ke taka rawa wajen nazarin yanayin ruwa, kiyaye albarkatun ruwa, da kuma magance matsalolin sauyin yanayi.

