Hedkwatar Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da sabuwar doka da ta haramta wa jami’an soji yin aure da ‘yan ƙasashen waje ko kuma da waɗanda suka zama ‘yan Najeriya ta hanyar samun takardar zama ɗan ƙasa.
Wannan mataki na cikin sabon tsarin aikin soja Wanda aka gyara a 2024 Kuma aka amince da shi bayan sa hannun Shugaban Ƙasa, tare da amincewar Majalisar Sojoji ta Ƙasa.
A cewar wannan doka, babu wani jami’i da ya halatta ya auri ɗan ƙasashen waje ko wanda ya zama ɗan ƙasa ta hanyar haƙƙin zama ɗan ƙasa.
Haka kuma, jami’an soji suna buƙatar neman izini daga manyansu kafin yin aure, inda dole a binciki wanda za su aura kafin a ba da amincewa.
Dokar ta kuma fayyace cewa, idan soja ya auri mace Yar kasar waje zai iya barin aiki,haka itama idan mace ta auri dan kasar waje, bisa yadda doka ta tanadar.
Rahoton ya bayyana cewa, an gabatar da wannan sabuwar doka ne domin kare tsaron ƙasa, inda wani tsohon janar (wanda bai so a bayyana sunansa ba) ya bayyana cewa aure da bakin mutum na iya zama barazana ga ɓoyayyun bayanan tsaro, musamman idan sojan yana aiki a wuri mai muhimmanci ko kuma kasar da matar ko mijin sa ta fito daga cikinta tana da hulɗa da Najeriya.
Sai dai wani tsohon jami’in Sojin Sama ya ce dokar na iya zama mai tsauri, yana mai cewa ya kamata a takaita ta ga waɗanda ke aiki a muhimman sassa na tsaro kawai, maimakon a hana duka jami’ai baki ɗaya.
Wasu daga cikin masu sharhi a ɓangaren farar hula sun bayyana cewa, duk da cewa manufar dokar na da kyau wajen kare martabar rundunar soji, yana da kyau a tabbatar da cewa ba ta tauye haƙƙin aure da walwalar jama’a ba.
Rahoton Leadership Newspaper ya ƙara da cewa, har yanzu ba a bayyana yadda wannan doka za ta shafi jami’an da suka riga suka auri ‘yan ƙasashen waje ba, ko kuma yadda za a aiwatar da ita a aikace.

