Kungiyar Masana kimayar Ruwa ta Najeriya, (NAHS), tayi gargaɗi kan yadda ake cike Kududdufai da tona Rijiyoyin Burtsatse barkai a Arewacin Najeriya,wanda hakan ke haifar da sauyin yanayin dake janyo karancin ruwa a da bushewar kasa.
Shugabanin Kungiyar ta NAHS sunyi wannan gargaɗin ne a yayinda Kungiyar ke gudanar da taronta na shekara karo na 15 a jami’ar Bayero da ke Kano, inda aka mayar da hankali kan mahimmancin ruwa da samar da wadataccen abinci duk da sauyin yanayin da ake fama dashi.
Taron, wanda ya tara masana,da jami’an gwannati da dalibai daga sassa daban-daban na ƙasar nan ,masana da dama zasu gabatar da mukala kan hanyoyin warware matsalolin sauyin yanayi dake janyo kamfar ruwa a yankuna dake fama da karancin ruwa.
A Jawabin Kungiyar masana kimiyar Ruwa ta Najeriya Farfesa O. D Jimoh ya bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta ɗauki matakan gaggawa wajen kare muhalli da kula da albarkatun ruwa, musamman ganin yadda sauyin yanayi ke haifar da ƙarancin ruwa da raguwa a samar da abinci.
Ya ce, “Ba za mu iya cimma samar da wadataccen abinci ba idan ba mu da tsarin sarrafa ruwa da ya dace”
Mataimakin Shugaban jami’ar Bayero Farfesa Haruna Musa wanda Shugaban sashen kula da dakunan Karatu na jami’ar Farfesa Kabiru Dahiru Abba ya wakilta ya nemi Masanan da su samarwa yankin Arewa mafita kan matsalolin da ake fama da su musamman sare bishiyoyi barkatai da da gurbata muhalli da sauransu.
Mai masaukin baki kuma Shugaban sashen ilimin nazarin Ƙasa na jami’ar Bayero sannan ma’ajin kuɗi na Kungiyar NAHS Farfesa Tasi’u Rulwanu Yalwa kira yayi ga gwamnati da ta ƙarfafa bincike da zuba jari a fannin ruwa da noman zamani.
Yace a wasu lokutan har karamar girgizar Ƙasa haka ke janyowa.
Haka kuma Farfesa Yalwa ya roki jama’a da gwamnatocin Arewa su daina yawan cike Kududdufai da tona Rijiyoyin Burtsatse barkai wanda ke janyo matsalolin da ba’a shirya musu ba.

