Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana godiya ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa irin tsayuwar da ya yi wajen sukar maganganun Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan Najeriya.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce abin da Kwankwaso ya yi alama ce ta kishin ƙasa da nuna son kare martabar Najeriya a idon duniya.
A cewar Onanuga, wannan lokaci ne da ya dace shugabannin siyasa su bar bambancin jam’iyyu su haɗa kai wajen kare mutuncin ƙasar.
“Mun gode wa Sanata Kwankwaso saboda irin kishin ƙasarsa da ya nuna. Wannan lokaci ne da ya dace shugabannin siyasa su haɗa kai wajen kare martabar Najeriya,” in ji shi.
Sanata Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) cewa kalaman Shugaba Trump masu cike da barazana kan Najeriya ba su da amfani kuma na iya tayar da hankulan jama’a.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci wadda matsalolin tsaronta ba su da alaka da addini, kabila ko siyasa.
Na lura da yadda Shugaba Trump ke ta yin maganganu masu tsanani kan Najeriya, musamman bayan ya sake sanya ƙasarmu cikin jerin ‘ƙasashen da ke da matsala ta addini’. Wannan ba daidai ba ne,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma shawarci gwamnatin Amurka da ta taimaka wa Najeriya ta hanyar fasahar zamani da bayanan sirri wajen yaƙi da ta’addanci maimakon yin barazana ko amfani da kalamai masu tayar da hankali.
TST Hausa ta rawaito cewa, Kwankwaso a martanin da ya mayarwa Shugaban kasar Amurika Donald Trump kan barazanarsa na kaiwa Najeriya hari,yace maimakon Trump din yayi barazanar kamata yayi ya taimaki Najeriya da kayan yaki na zamani domin kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya
A ƙarshe, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ƙara ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da ƙasashen duniya ta hanyar naɗa jakadu da wakilai na musamman, yana mai kiran ‘yan Najeriya da su haɗa kai domin kare martabar ƙasar.

