Masana’antar Kannywood ta sake shiga jimami bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun jarumanta, Malam Nata’ala, wanda aka fi sani da Mato Na Mato a cikin shirin Dadin Kowa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Malam Nata’ala ya rasu ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan doguwar fama da rashin lafiya da ake dangantawa da ciwon daji.
A cikin watannin baya, an ga jarumin cikin wani bidiyo yana neman taimakon jama’a domin samun kudin magani. Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin kula da lafiyarsa, yayin da wasu shugabanni da ‘yan kasuwa suka taimaka wajen ganin ya samu sauƙi.
Sai dai duk da irin wannan taimako, Allah Ya ƙaddara rasuwarsa, abin da ya jefa ‘yan fim da masoyansa cikin alhini da jimami.
Tsohon abokin aikinsa a Kannywood ya bayyana cewa, “Malam Nata’ala mutum ne mai barkwanci da natsuwa, wanda ya shahara wajen kawo dariya a fina-finai amma yana da ɗabi’a ta ladabi da biyayya.”
Bayanai sun nuna cewa ana shirye-shiryen gudanar da jana’izarsa, kodayake har yanzu ba a bayyana ainihin wurin da za a binne shi ba.
Allah Ya jikansa, Ya ba iyalansa da abokan aikinsa haƙuri da juriya, Ya kuma gafarta masa kurakuransa.

