Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe sama da naira biliyan uku (₦3,000,000,000) domin aiwatar da muhimman ayyuka na inganta samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya shaida hakan a taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa karo na 33 wanda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.
Kwamishinan za’a yi amfani da kudaden wajen gyaran tsofaffin bututun ruwan sha, da gina sabbin injinan tace ruwa a wasu yankuna musamman Rano da ake fama da matsalar ƙarancin ruwa,da kuma wasu wurare a cikin birnin Kano.
Ya ce gwamnatin ta himmatu wajen tabbatar da manufar kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwa da jama’a ke fuskanta a lokuta da dama, tare da tabbatar da cewa kowace unguwa ta samu isasshen ruwa mai tsafta.
Kwamred Wayya yace gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga ayyukan da suka shafi jin daɗin jama’a, kamar samar da ruwa,da lafiya,da ilimi da ingantacciyar rayuwa.
TST Hausa ta rawaito cewa zaman majalisar zartaswar ya amince a Kashe kuɗi sama da naira miliyan dubu 19 a ayyukan da aka amince da aiwatarwa.

