Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin ganawa da Shugaban Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan dambarwar Difilomasiya tsakanin kasashen biyu musamman zargin kisan Kiristoci a sassan Najeriya,da Amurika.
Rahoton da jaridar Daily Post Nigeria ta wallafa ya nuna cewa ganawar za ta mayar da hankali ne kan batun kare ‘yancin addini, da tabbatar da zaman lafiya da adalci, tare da ƙarfafa hulɗar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka.
Wata majiya ta bayyana cewa ganawar na cikin wani shiri na tsare-tsaren tattaunawa tsakanin manyan shugabanni na kasashen duniya kan batutuwan tsaro, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
An ce Tinubu zai bayyana wa Trump irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen shawo kan rikice-rikicen addini da na kabilanci a ƙasar.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban ƙasa ko daga gwamnatin Amurka da ta tabbatar da ranar ko wurin da za a gudanar da ganawar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na iya zama wani ɓangare na yunƙurin Tinubu na gyara huldar Najeriya da wasu manyan ƙasashen duniya bayan wasu ƙuntatawar da aka samu a dangantakar diflomasiyya a watannin baya.
Masu nazari a fannin siyasa na ganin cewa ganawar Tinubu da Trump idan ta tabbata za ta iya zama wata dama ta sake jan hankalin Amurka kan batun tsaro da ‘yancin addini a Najeriya, musamman ganin yadda ake ta samun suka daga kungiyoyin Kiristoci da masu fafutuka kan kare hakkokin ɗan adam.
A halin yanzu dai, ana sa ran gwamnatin Najeriya za ta fitar da cikakken bayani domin fayyace gaskiyar lamarin da kuma abin da ake sa ran cimmawa a wannan ganawar mai muhimmanci.

