Wasu ‘yan bindiga sun sace mataimakin Shugaban majalisar dokokin Jihar Kebbi, Hon. Samaila Bagudu, a garinsa na Bagudu, da ke cikin karamar hukumar Bagudu ta Jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne , lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye garin Bagudu, inda suka fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, kafin su yi awon gaba da mataimakin kakakin, jim kadan bayan ya fito daga masallaci bayan sallar Juma’a.
Mai magana da yawun Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da wanda aka sace cikin koshin lafiya.
Sai dai, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da karin bayani ba kan yadda lamarin ya faru, ko matakan da ake dauka don ceto wanda aka sace.
Wannan sace-sacen na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman ma a Jihar Kebbi, inda ake yawan samun hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane domin neman kudin fansa.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa satar jami’in gwamnati a irin wannan matsayi na nuna yadda barazanar tsaro ke kara taɓarɓarewa a yankin, tare da bukatar daukar gaggawar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

